Sir Ahmadu Muhammadu Bello (Ahmadu Bello an haife shi ne a 12 ga watan June shekarar alif 1910,a ƙaramar hukumar Raba dake jihar Sakkwato)[1] KBE ko Sardauna shine tsohon Firimiyan Arewacin Najeriya kuma ya rike sarautar Sardaunan a jihar Sakkwato. An haifi Sir Ahmadu Bello sardauna a garin Raba dake cikin lardin Sakkwato a shekara ta alif dubu ɗaya da ɗari tara da goma (1910). A shekarar alif ɗari tara da arba'in da tara, 1949 ya sami zuwa majalisar dokoki ta jihar Arewa, yana kuma daga cikin mutum na uku da aka zaɓa acikin ƙungiyar da ta rubuta sabon kundin tsarin mulkin ƙasar.[2]Sardauna ya kasance wani mutumi ne dake da mahimmanci sosai ga mutanen arewacin Najeriya, dama faɗin ƙasar gaba ɗaya, saboda irin ayyukan cigaba daya ƙirƙiro a yankin arewa harma da kudancin ƙasar gaba ɗaya. Kamar jami'ar Ahmadu Bello, Gidan Rediyo dake jihar Kaduna, da sauransu. Duk da cewa Sardaunan sokoto Sarauta ce tashi a Jihar Sokoto, Amma sunan ya zama kamar wani inkiya a gareshi inda ya shahara wajen amsa shi a ciki da wajen Najeriya.
Ahmadu Bello: Sardauna of Sokoto
2ff7e9595c
Comments